Zaben gwarzuwar 'yar kwallon kafar BBC

Image caption 'Yar wasan Kamaru Gaelle Enganamouit na cikin wadanda za su fafata.

An bayyana sunayen mutum biyar da za su fafata domin cin gasar "gwarzuwar" 'yar kwallon kafar BBC ta shekarar 2016.

'Yan wasan su ne:'yar wasan Kamaru Gaelle Enganamouit, 'yar wasan Faransa Amandine Henry, Kim Little daga Scotland da kuma'yan wasan Amurka Carli Lloyd da Becky Sauerbrunn.

Za a fara zaben ne a shafin intanet na BBC ranar Litinin, tara ga watan Mayu da karfe 08:00 na safe a agogon GMT.

Za ku iya kada kuri'arku a nan: http://www.bbc.co.uk/sport/live/football/36049248

Enganamouit, wacce ke buga wasa a kulob din Eskilstuna United na kasar Sweden, tana cikin 'yan wasan Kamaru da suka kai kasar cikin kungiyoyi 16 da za su fafata a gasar cin kofin duniya a bara.