Mahrez ya lashe gasar PFA

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mahrez ya zura kwallo 17 a wasan lig-lig da ya buga wa Leicester.

Dan wasan gaba na Leicester City Riyad Mahrez ya lashe gasar gwarzon dan kwallon kafa na "Kungiyar masana wasan kwallon kafa" ta bana.

Mahrez ya zura kwallo 17, sannan ya taimaka aka zura kwallo 11 a wasan lig-lig 34 da ya buga wa Leicester.

Dan wasan tsakiya na Tottenham Dele Alli, mai shekara 20 ne ya lashe gasar ta bana a rukunin "kananan 'yan wasa", yayin da 'yar wasan Manchester City Izzy Christiansen ta lashe gasar a rukunin mata.

'Yar wasan gaba ta Sunderland Beth Mead, mai shekara 20 ce ta lashe gasar gwarzuwar 'yar wasa ta bana a rukunin "kananan 'yan wasa mata".

Mahrez, mai shekara 25, ya fafata ne da Harry Kane, Mesut Ozil, Dimitri Paye, Jamie Vardy da kuma N'Golo Kante.