Manchester City za ta kara da Real Madrid

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption City da Madrid sun taba karawa a gasar zakarun Turai a 2012

Manchester City za ta karbi bakuncin Real Madrid a gasar cin kofin zakarun Turai a wasan daf da na karshe ranar Talata a Ettihad.

Real Madrid, wadda ta lashe kofin zakarun sau 10, ta kai wasan daf da na karshe ne bayan da ta doke Wolfsburg da ci 3-2 a wasanni biyu da suka kara.

Ita kuwa Manchester City wadda ba ta taba daukar kofin ba, ta kai wasan daf da na karshe ne, bayan da ta ci PSG 3-2 a wasa biyun da suka fafata.

Manchester City ta kara da Real Madrid sau biyu a baya a gasar ta zakarun Turai, inda wasan farko Real Madrid ta ci City 3-2 ranar 18 ga watan Satumbar 2012.

Fafatawa ta biyu kuwa da suka yi a Ettihad, kungiyoyin biyu tashi wasa suka yi kunnen doki 1-1 a ranar Laraba 21 ga watan Nuwambar 2012.