West Ham za ta fafata da Juventus

Hakkin mallakar hoto epa
Image caption Juventus na daf da lashe kofin Seria A na shekarar nan

West Ham United ta shirya buga wasan sada zumunta da Juventus, domin bikin bude sabon filin wasanta mai suna Olympic ranar 7 ga watan Agusta.

West Ham wadda ke yin wasanninta a Upton Park shekara 112, za ta koma sabon filin ne da zai ci 'yan kallo 60,000 wanda aka gina a shekarar 2012, saboda wasannin Olympics da Landan ta karbi bakunci.

Juventus wadda ta lshe kofin zakarun Turai karo biyu, na daf ta lashe kofin Seria A na bana kuma na biyar a jere.

Wannan ne kuma karon farko da kungiyoyin biyu za su fafata a tsakaninsu.