Wolfsburg ta raba gari da Bendtner

Hakkin mallakar hoto Reax Features
Image caption Sauran shekara daya kwantiragin Nicklas Bendtner ya kare a Wolfsburg

Wolfsburg ta kawo karshen yarjejeniyar da ta kulla da Nicklas Bendtner, duk da saura shekara daya ta cika.

Rabon da Bentner, mai shekara 28, dan kasar Denmark ya yi wasa tun cikin Fabrairu, kuma a watan jiya aka ce masa kada ya kara zuwa sansanin horon 'yan wasa.

A cikin watan na Maris kungiyar ta ci tarar dan wasan, sakamakon makara zuwa atisaye da ya yi na tsawon minti 45.

A kuma cikin watan Fabrairu aka hukunta shi, bayan da ya saka hoton sabuwar motarsa kirar kamfanin Mercedes a shafinsa na sada zumunta, bayan da Volkswagen ne ke daukar nauyin Wolfsburg.

Bentner ya koma Jamus da murza leda a cikin watan Agustan 2014 daga Arsenal, sannan ya buga wasanni 31, inda ya ci kwallaye uku kacal.