Za a dakatar da Dele Alli daga buga wasa

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Alli yana da matukar tasiri a wasanni da Tottenham ke murzawa.

Dan wasan tsakiya na Tottenham Dele Alli yana fuskantar dakatarwa daga buga wasanni uku bayan wani hoton bidiyo ya nuna shi yana naushin dan wasan West Brom Claudio Yacob a ciki.

Talli ya naushi Yacob a lokacin wasan da suka tashi da ci 1-1 ranar Litinin.

Mai yiwuwa hukumar kwallon kafar Ingila za ta yanke hukuncin cewa abin da ya yi yana da matukar illa.

Wasan da suka yi na ranar Litinin ya yi kafar-ungulu ga yunkurin da Tottenham ke yi na lashe kofin Premier a bana.

Kociyan Tottenham Mauricio Pochettino ya ce bai ga lokacin da Alli ya naushi Yacob ba, ko da ya ke ya kara da cewa, "A wasu lokutan abokan hamayyarmu suna taƙalarsa domin su fusata shi ganin cewa shi dan wasa ne da ba ya son raini".

Alli yana da matukar tasiri a wasanni da Tottenham ke murzawa tun lokacin da ya fara taka leda a kakar wasa ta bana.

Ya zuwa yanzu, ya zura kwallo 10 kuma yana taimakawa takwaransa na kulob din Harry Kane domin zura kwallaye.