Zan auna makomata a Liverpool - Toure

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kolo Toure tsohon dan wasan Arsenal da Manchester City

Kolo Toure ya ce zai ci gaba da taka leda a Liverpool idan da gudunmawar da zai bai wa kungiyar.

Yarjejeniyar da Toure mai shekara 35 ya kulla da Liverpool zai kare ne a karshen kakar wasannin bana, sai dai kuma koci Jurgen Klopp ya ce yana bukatar dan wasan.

Toure ya shaida wa BBC cewar abin farin ciki ne ka ji wadannan kalaman daga fitatcen mai horarwa, amma zai duba makomarsa a Anfield din.

Dan wasan dan kasar Ivory Coast ya buga wa Liverpool karawar da suka tashi 2-2 da Newcastle a gasar Premier inda ya maye gurbin Mamadou Sakho.

Sakho bai buga wasan ba ne saboda bincikensa da hukumar kwallon kafar Turai ke yi kan shan kwayoyi masu kara kuzari.