An hukunta Norwich da Sunderland

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption An yi wasanni 35 a gasar Premier ta bana

Hukumar kwallon kafa ta Ingila ta ci tarar Norwich da Sunderland kudi fam 30,000 kowaccensu, sakamakon kasa tsawatar wa 'yan wasansu a gasar Premier.

Kungiyoyin biyu sun kara ne a wasan gasar Premier a ranar 16 ga watan Afirilu, kuma Sunderland ce ta ci wasan 3-0.

Sai dai kuma tun farkon fara karawar 'yan wasan da jami'an kungiyoyin biyu suka dunga mayar wa da juna kalamai daf da bakin filin wasa.

Norwich ba ta amince da tuhumar da FA ta yi mata ba tun farko, inda Sunderland ta ce ta yi laifin da bai kamata ba.

Norwich tana mataki na 18 a kan teburi da maki 31, yayin da Sunderland ita ma ke da maki 32 a matsayi na 17.