Madrid na kara habaka karkashin Zidane

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Sauran wasanni uku suka rage a kammala gasar La Liga ta bana

Gareth Bale ya ce Real Madrid na kara habaka karkashin jagorancin koci Zinedine Zidane.

Bale tsohon dan wasan Tottenham ya kara da cewar Zidane ya san tamaula, yana kuma barin 'yan wasa su nuna kwarewarsu yayin da ake taka leda.

Zidane ya karbi aikin horar da Real Madrid daga hannun Rafael Benitez a cikin watan Janairu.

Real Madrid ta kai wasan daf da karshe a gasar cin kofin zakarun Turai, tana kuma mataki na uku a teburin La Liga biye da Barcelona da Atletico Madrid.

Zidane ya lashe kofin duniya a matsayin dan wasan tamaula, ya kuma karbi kyautar gwarzon dan wasan kwallon kafa na duniya sau uku.

A makon jiya ne Zidane ya ce Gareth Bale mai ban mamaki ne a fagen tamaula kuma kwararren dan wasa ne.