An dakatar da kociyan Atletico Madrid

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Diego Simeone zai jagoranci Atletico wasan da za ta yi da Bayern Munich

An dakatar da kociyan Atletico Madrid, Diego Simone, daga jan ragamar kungiyar a wasanni uku da suka rage na gasar La Liga Spaniyar bana.

An sami kociyan, mai shekara 45, da laifin umartar mai dauko kwallo da ya jefa ta cikin fili lokacin da Malaga ta kai hari garin Atletico.

Kungiyoyin biyu sun buga gasar La Liga wasan mako na 35 a ranar Asabar, inda Atletico ta ci wasan da ci daya mai ban haushi.

Kociyan ba zai jagoranci wasan da Atletico za ta yi da Rayo Vallecano ranar 30 ga watan Afirilu da Levante ranar 8 ga watan Mayu da wasan karshe ranar 15 ga watan Mayu da Celta Vigo.

Kociyan zai jagoranci wasan gasar cin kofin Turai da Atletico za ta yi da Bayern Munich a wasan daf da na karshe.