Enyimba da Heartland sun tashi 1-1

Hakkin mallakar hoto HeartlandFC twitter
Image caption An buga wasannin mako na 13 a gasar Firimiyar Nigeria

Enyimba da Hertland sun tashi wasa canjaras 1-1 a kwantan wasan Firimiyar Nigeria da suka kara a ranar Laraba.

Enyimba ce ta fara cin kwallo ta hannun Peter Onyekachi a minti na 27 da fara tamaula, bayan da mai tsaron ragar Heratland ya bashi tamaula kyauta.

Heartland ta farke kwallon da aka zura mata ne saura minti 14 a je hutun rabin lokaci ta hannun Ifeanyi Onuigbo.

Kungiyoyin biyu sun buga kwantan wasan mako na shida da ba su yi ba a baya, sakamakon kofin zakarun Afirka da Enyimba ke yi.

Ita kuwa Sunshine Stars 3-0 ta ci Nasarawa United a kwantan wasan mako na bakwai da suka yi a Akure a ranar ta Laraba.