Ba ma jin tsoron Real Madrid — Pellegrini

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Samir Nasri ba ya cikin tawagar da za ta buga gasar Zakarun Turan.

Kociyan Manchester City Manuel Pellegrini ya ce ba sa jin tsoron sake karawa da Real Madrid a a zagaye na biyu na wasan dab da na karshe na cin kofin Zakarun Turai da za su yi duk da cewa David Silva ba zai buga wasan ba.

City, wadanda ke fatan kai wa wasan karshe na gasar a karon farko, sun tashi 0-0 a karawarsu ta farko da Madrid a Etihad.

Silva ba zai buga wasan, wanda za a yi ranar hudu ga watan Mayu ba, saboda raunin da ya ji a cinyarsa.

Pellegrini ya ce, "Ba na tsoron Real. Ba ma tsoron fafatawa da su a filin wasa na Bernabeu."

Real dai ba su sha kaye a wasannin Zakarun Turai da suka buga a gida ba, tun da aka fara kakar wasa ta bana.

City dai za su bugawa wasan ne ba tare da Yaya Toure ba saboda raunin da ya ji, yayin da ba a sa Samir Nasri a cikin tawagar da za ta buga gasar Zakarun Turan ba.