Madrid za ta kai wasan karshe - Bale

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Real Madrid ta lashe kofin zakarun Turai sau 10 jumulla

Gareth Bale ya ce Real Madrid za ta kai wasan karshe a gasar cin kofin zakarun Turai ta bana.

Manchester City da Real Madrid sun tashi wasa babu ci 0-0 a karawar da suka yi a ranar Talata a Ettihad.

Bale ya buga wasansa na farko a Ingila, wanda rabonsa da taka leda a kasar tun barinsa Tottenham a 2013.

Real Madrid wadda ta lashe kofin zakarun Turai sau 10, za ta karbi bakuncin Ettihad a wasa na biyu a ranar 4 ga watan Mayu.