Dele Alli ba zai buga wasanni uku ba

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Alli ba zai sake buga wasa ba a kakar wasa ta bana.

Dan wasan Tottenham Dele Alli ba zai buga wasanni ukun da suka ragewa kulob dinsa ba a gasar Premier, sakamakon hukuncin da hukumar kwallon kafar Ingila ta yanke masa kan nuna rashin da'a.

Alli dai ya naushi dan wasan West Brom, Claudio Yacob a ciki, a wasan da suka tashi 1-1 ranar Litinin, ko da ya ke alkalin wasa bai bayar da labarinsa ba.

Amma hoton bidiyon da aka dauka na wasan ya nuna Alli yana naushin Yacob.

Kociyan Tottenham Mauricio Pochettino ya ce bai ga lokacin da Alli ya naushi Yacob ba, ko da ya ke ya kara da cewa, "A wasu lokutan abokan hamayyarmu suna taƙalarsa domin su fusata shi ganin cewa shi dan wasa ne da ba ya son raini".