Liverpool za ta biya £8m kan Ings

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Tsohon dan wasan Burnley, Danny Ings

Wata kotun musamman ta umarci kungiyar wasa ta Liverpool da ta biya kulob din Burnley diyya ta Fam miliyan 8, kan komawar Danny Ings zuwa Liverpool.

Fam miliyan 6.5 daga cikin kudin na zaman dan wasan ne a Burnley, a inda kuma Fam miliyan 1.5 suka kasance na 'yan kunji-kunji.

Ings, mai shekara 23, ya bar Burnley ne zuwa Liverpool a karshen kakar bara, bayan da kwantaraginsa ya kare.

Sakamakon rashin cimma matsaya kan diyyar da za a biya ne yasa kotun ta musamman ta shigo cikin al'amarin.