Leicester za ta iya daukar kofi — Mandaric

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Milan Mandaric, tsohon mai kulob din Leicester

Tsohon mai kulob din Leicester City, Milan Mandaric ya ce nasarorin da kungiyar take samu za su dore.

Idan dai har Leicester ta doke Manchester United a wasan da za su yi rananr Lahadi, to za ta dauki kofin gasar Premier na farko tun kafa kungiyar shekaru 132 da suka gabata.

A 2010 ne dai Mandaric, mai shekara 77, ya sayar da kulob din na Leicester.

Mandaric ya ce "babu mamaki duk abin da aka kungiyar za ta yi, kamar dai yadda na san su."

Leicester City dai tana saman teburin gasar Premier kuma maki 3 kawai take nema ta ciwo kofin na Premier, a wasannin ukun karshe da suka rage mata.