Uefa: An dakatar da Sakho kan ƙwaya

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Mamadou Sakho, dan wasan baya na Liverpool

Hukumar kwallon kafa ta Turai Uefa ta dakatar da dan wasan baya na Liverpool, Mamadou Sakho har na kwanaki 30 saboda an gano yana shan kwaya.

Hukumar ta Uefa dai ta fara wani bincike ne a kan dan wasan tun bayan da ya gaza haye gwajin gano masu shan kwaya mai kara kuzari.

Dakatarwar ta wicin gadi ce, kafin sashen kula da ɗa'a na hukumar ta Uefa ya ɗauki matsaya.

An dai gano cewa Sakho, mai shekara 26, yana shan wata ƙwaya wadda ake kyautata zaton ta markaɗe kitse ce daga jiki, bayan wasan da suka yi da Manchester United, ranar 17 ga Maris.