Europa: Villareal ta ci Liverpool 1-0

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption An kwashe fiye da minti 90 ba tare da ci ba.

Kungiyar wasa ta Villareal ta jefa kwallo daya mai ban haushi a ragar Liverpool, a gabar farko ta wasan kusa da na karshe na gasar zakarun turai ta Europa.

An dai kwashe fiye da minti 90 ana fafatawa ba tare da cin kwallo ba.

Amma dan wasan Villareal, Andrian Lopez ya samu ya zura kwallo a ragar ta Liverpool a minti na 92.

Yanzu dai Villareal ce za ta ziyarci Liverpool domin buga bangare na biyu na wasan.