Platini ya kai kara kan dakatar da shi

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption An dakatar da Blatter da Platini daga shiga harkokin wasa.

Shugaban Uefa Michel Platini ya daukaka kara kan dakatarwar da hukumar kwallon kafar duniya Fifa ta yi masa daga harkokin wasanni na tsawon shekara shida.

A bara ne Fifa ta dakatar da shugabanta Sepp Blatter da Platini daga shigar harkokin wasanni bayan an same su da hannu a wata cuwa-cuwa da ta kai $2m.

Mutanen sun musanta aikata laifin.

Amma Platini ya kai Fifa gaban kotun da ke sasantawa kan harkokin wasanni da ke Switzerland, kuma da alama a makon gobe za ta yanke hukunci.