Serena ta fice daga gasar Madrid Open

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Serena ta yi fafata a gasa hudu tun watan Agustan bara amma ba ta yi nasara ko sau daya ba

Fitacciyar 'yar wasan tennis Serena Williams ta fita daga gasar Madrid Open saboda mura da take fama da ita.

Agnieszka Radwanska ta maye gurbinta a matsayin fitacciyar 'yar wasa da za ta fafata a gasar, yayin da Serena kuma take daf da fara kakar wasan tennis da ake yi a turbaya a birnin Rome.

'Yar wasan mai shekara 34 ta yi wasanni a gasa hudu tun watan Agustan bara, inda kuma ba ta yi nasara ko sau daya ba.

Za a fara wasan gasar Madrid Open ne a ranar Asabar.