Ni nasa aka gina filin Emirate — Wenger

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Kociyan Arsenal, Arsene Wenger

Kociyan Arsenal, Arsene Wenger ya ce saboda irin kokarinsa ne ya sanya bankuna suka ba wa kungiyar wasan rancen kudaden da ta gida filin wasanta na Emirate.

Magoya bayan kulob din dai sun kudiri niyyar yin zanga-zanga saboda rashin taka muhimmiyar rawa da kungiyar ta Arsenal ta yi a kakar bana.

Arsene Wenger ya ce " Lokacin da muka gina filin wasan, bankuna sun nemi da na rattaba hannun kan yarjejeniyar shekara 5."

Ya kara da tambayar cewa " Kana son sanin kungiyoyin wasa nawa naki zuwa a wannan lokacin?"

An dai fara gina filin wasan ne na Emirate a kan kudi £390m, a 2004, a shekarar da Wenger ya daukowa kulob din kofi Premier na uku.