Newcastle ta tsallake siratsi

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Andros Townsend yana buga kwallo

Kungiyar wasa ta Newcastle ta tsallake rijiya da baya daga fita daga gasar Premier bana.

Dan wasan Newcastle Townsend ne ya jefa kwallo daya mai ban haushi a ragar Crystal Palace, a wasan da suka yi, ranar Asabar.

Crystal Palace ta samu bugun fanaret amma dan wasanta, Yohan Cabaye ya zubar.

Yanzu haka, Newcastle ce ta 17 a teburin gasar ta Premier.