Juventus ta ci wasa na 10 a jere

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Juventus za ta dauki kofin Serie A karo na biyar a jere.

Kungiyar wasa ta Juventus ta lallasa Carpi da 2-0 a wasan da suka yi da yammacin Lahadi.

'Yan wasan kulob din, Hernanes da Simone Zaza ne suka jefa kwallayen, a lokacin wasan wanda shi ne karo na 10 da kulob din yake samun nasara a jere.

Daman dai tun ranar Litinin ne Juventus ta samu damar daukar kofin gasar Serie A, bayan da mai biye mata a baya, Napoli ta kasa yin nasarar a wasan da ta yi da Roma.

A ranar 21 ga Mayu ne dai Juventus za ta buga wasan karshe da AC Millan.

Wannan shi ne karo na biyar a jere da kulob din yake lashe kofin gasar.