Sadio Mane ya ci Man City kwallaye uku

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Dan wasan Southampton, Sadio Mane

Dan wasan Southampton, Sadio Mane ya zura kwallaye uku a ragar Manchester City, a wasan da suka tashi 4-2, ranar Lahadi.

Hakan dai na nuna rashin tabbas ga burin Man City na samun gurbin buga gasar zakarun Turai.

Yanzu haka dai maki biyu ne tsakanin Southampton da mai mataki na shida wato West Ham, kuma za ta iya samun damar buga gasar Europa ta badi.

Ita kuma Man City, har yanzu ita ce ta hudu a teburin Premier sannan akwai tazarar maki 4 tsakaninta da Manchester United, mai mataki na biyar.