Reniero ba zai kalli wasan Chelsea da Tottenham ba

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Mista Ranieri yana sa ran daukar kofin gasar Firimiyar Ingila

Mai yiwuwa kociyan Leicester Claudio Ranieri ba zai kalli wasan da za a fafata tsakanin Chelsea da Tottenham ba a ranar Litinin, saboda zai kasance kan hanyarsa ta dawowa daga Italiya.

Kulob din nasa na Leicester zai samu nasarar lashe gasar Firimiyar Ingila in har Chelsea ta ci Tottenham.

Mista Ranieri ya ce, "Zan so na kalli wasan Tottenham amma kuma hakan ba zai samu ba, saboda ina son in ci abincin rana da mahaifiyata mai shekara 96."

Ya kara da cewa, "Zuciyata na gaya min, Tottenham za ta yi nasarar dukkan wasannin uku. Yanzu na fi mayar da hankali ne kan wasan Everton. Dole mu cigaba da mayar da hankali."