FA za ta hukunta Fellaini da Huth

Image caption Dan wasan Leicester, Robert Huth

Hukumar kwallon kafar Ingila, FA, tana tuhumar dan wasan Manchester United na tsakiya, da mai tsaron Leicester, Robert Huth kan fada a lokacin wasa.

Fellaini dai ya kaiwa Huth naushi sakamakon riko gashinsa da Huth din yayi, a wasa da suka tashi 1-1 a Old Trafford.

Sai dai kuma alkalan wasa ba su ga lokacin da hakan ta faru ba amma hotunan bidiyo sun tabbatar da hakan.

Hukumar ta FA za ta iya dakatar da 'yan wasan su biyu daga buga wasanni har uku, amma an ba su har zuwa ranar Laraba, 4 ga Mayu domin yin bayani kan hakikanin abin da ya faru.