Mousa Dembele ka iya fuskantar dakatarwa

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Dembele a lokacin da ya yakushi Diego Costa

Dan wasan Tottenham na tsakiya, Mousa Dembele ka iya fuskantar dakatarwa saboda yakushin idon dan wasan Chelsea, Diego Costa da ya yi a lokacin wasan da suka tashi 2-2 a Stamfarod Bridge.

Hotunan talbijin ne dai suka fallasa dan wasan, a lokacin da yake tsokanewa Costa idanu.

Duk da cewa mai busa wasa bai hukunta dan wasan ba, hukumar kwallon kafar Ingila za ta iya daukar mataki domin hana afkuwar haka a gaba.

A makon da ya gabata ne kuma aka dakatar da dan wasan na Tottenham, Dele Alli, daga buga wasanni uku sakamakon naushin dan wasan West Brom, Claudio Yacon, da ya yi a ciki.