Yadda na ji da Leicester ta dauki kofi — Ranieri

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Magoya bayan Leicester cikin murna

Kociyan Leicester City, Claudio Ranieri ya ce yana matukar farin ciki mara misaltuwa kan yadda ya jagoranci kulob din har ya dauki kofin farko a tsawon tarihin kungiyar.

A ranar Litinin ne dai aka tabbatar cewa Leicester ce za ta dauki kofi, bayan kunnen doki wato 2-2 da Tottenham, mai biye mata, ta yi da Chelsea.

Ranieri wanda ya fara horas da 'yan wasan kulob din na Leicester a watan Yulin 2015 ya ce "ina matukar alfahari da wannan al'amari."

Ya kara da cewa " 'yan wasan su yi rawar gani domin kokarinsu da jajircewarsu ne suka sa aka kai ga nassara."

Ranieri dai ya kasance tare da mahaifiyarsa a Italiya, kafin daga bisani ya dawo Ingila domin ya kalli wasan na Chelsea da Tottenham.