Yaya Toure ya koma atisaye

Dan wasan Manchester City Yaya Toure ya yi atisaye gabanin karawar da za su yi da Real Madrid a zagaye na gasar cin kofin Zakarun Turai.

Toure bai buga wasanni biyu da suka gabata ba, cikinsu har wanda suka yi 0-0 saboda raunin da ya ji a cinyarsa.

Su ma Samir Nasri David Silva ba su buga wasannin ba saboda jinyar da suke yi.

Kocin City Manuel Pellegrini ya zabi yin atisaye a filin wasan na Manchester gabanin tafiyarsu Madrid.