Jeffrey Webb zai fuskanci fushin Fifa

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Jefferey Webb, ya fito daga tsiburin Cayman

Tsohon shugaban hukumar kwallon kafa ta duniya, Fifa, Jeffey Webb yana fuskantar dakatarwa daga harkokin wasan kwallon kafa, sakamakon bincike da kwamitin da'a na hukumar ya fara, a kansa.

A watan Nuwamba ne, Webb, mai shekara 51, ya amsa daya daga cikin laifukan da ake tuhumar sa da su.

Ana dai tuhumar Webb ne da laifuka da suka jibanci hada kai domin yin cuwa-cuwa da safarar kudade.

Mista Webb na daya daga cikin mutanen da aka tsare a Zurich, a watan Mayun bara, kafin gudanar da taron hukumar Fifa, a birnin.