Zai wuya a samu kamar Leicester — Ranieri

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Magoya bayan kungiyar Leicester

Kociyan Leicester, Claudio Ranieri ya ce zai yi wuya wata kungiyar wasa maras kudi ta sake lashe kofin Premier, a nan gaba.

An yi wa 'yan wasan Leicester gaba dayansu kudi kan £57m, abin da ke nuna cewa su ne 'yan wasan da suka fi na kowane kulob araha, a gasar Premier Ingila ta bana.

Ranieri ya ce " Kudi ne ka sa a samu 'yan wasa masu kyau, kuma 'yan wasa masu kyau ne suke cin wasanni a yawancin lokuta."

Ya kara da cewa " Abin da zai faru ke nan a kakar wasanni mai kamawa, kai har ma nan da shekara 10 ko 20."

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wani mai goyan bayan Leicester

Wani bincike ya nuna cewa Tottenham ta hada 'yan wasanta a £159m, a inda Arsenal ta kashe £231m, ita kuma Liverpool ta hada 'yan wasanta a kan £260m, yayin da Chelsea kuma ta zuba £280.

Manchester United ta sanya £395m, a inda Manchester City kuma ta kashe £415m.

Ranieri ya ce nasara irin wadda Leicester ta samu ta daukar kofin Premier, na zuwa ne sau daya a shekara 20.

A shekarar 1978 ne kungiyar wasa ta Nottingham Forest ta lashe kofin Premier, sannan Blackburn Rovers ma ta samu wannan nasarar a 1995.