Uefa: Real Madrid ta doke Man City

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Real Madrid za ta kara da Atletico Madrid a wasan karshe

Kungiyar Real Madrid ta doke Manchester City da ci 1-0, a wasan zango na biyu na wasan kusa da karshe na gasar zakarun Turai da suka yi da yammacin Laraba.

Dan wasan Real Madrid, Gareth Bale ne dai ya jefa kwallon daya tilo minti 20 da fara wasa.

Yanzu haka, Real Madrid za ta fafata da Atletico Madrid a wasan karshe da za a yi ranar 28 ga Mayu.

A ranar Talata ne Atletico Madrid ta cancanci buga wasan karshe, bayan doke Bayern Munich a gidanta.