Tennis: Murray ya doke Gilles Simon

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Andy Murray ne mai rike da kambun gasar kwallon Tennis.

Mai rike da kambun gasar tenis ta duniya Andy Murray ya cancanci zuwa wasan dab da na kusa da na karshe na gasar Tennis da ta Madrid Open da ake yi a birnin Madrid na Spaniya.

Dokewar da Murray ya yiwa Gilles Simon da ci 6-4 da 6-2 ce ta bashi damar kaiwa ga gaci.

Andy ya ci duka bugun kwallayensa sannan kuma gwanintar da ya nuna ta fi karfin Simon mai shekara 31.

Andy Murry, mai shekara 28, wanda shi ne mai matsayi na biyu a gasar kwallon tennis a duniya, zai fafata da Tomas Berdych, dan jamhuriyar Cek.