FA ta dakatar da Fellaini da Huth

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Dan wasan Leicester, Roberto Huth na daya daga cikin wadanda aka dakatar

Hukumar kwallon kafar Ingila, FA, ta dakatar da dan wasan Manchester United na tsakiya, Marouane Fellaini da dan bayan Leicester, Robert Huth, daga wasanni uku kan fada a lokacin wasa.

Fellaini dai ya kaiwa Huth naushi sakamakon riko gashinsa da Huth din yayi, a wasa da suka tashi 1-1 a Old Trafford.

Sai dai kuma alkalan wasa ba su ga lokacin da hakan ta faru ba amma hotunan bidiyo sun tabbatar da hakan.

Yanzu haka, Fellaini ba zai buga wasannin da suka ragewa Manchester United ba, amma zai taka ledar da kulob din zai yi da Crystal Palace a wasan karshe na FA Cup, ranar 21 ga Mayu, a Wembley.

A inda shi kuma Huth ba zai buga wasanni biyun da suka ragewa Leicester ba da suka hada da wasan karshe, sannan kuma ba zai buga wasan farko ba na gasar Premier ta kaka mai kamawa.