Europa: Liverpool za ta kara da Sevilla

Image caption Liverpool ta ci Villareal 3-0

Kungiyar Liverpool za ta kara da Sevilla, a wasan karshe na gasar Europa, bayan da ta doke Villareal da ci 3-0, a zango na biyu na wasan kusa da karshe.

Dan wasan Villareal, Soriano ne ya fara cin kungiyar wasansa da kansa, kafin 'yan wasan Liverpool, Daniel Sturridge da Adam Lallana su jefa kwallo ta biyu da ta uku.

A zangon farko dai na wasan na kusa da karshe, Villareal ce ta jefawa Liverpool kwallo daya mai ban haushi a raga.

Ke nan an tashi wasa 3-1 a jumullar kwallayen da kungiyoyin suka ci a wasanninsu biyu.

Ita ma Sevilla da 3-1 ta doke Shakhtar Donesk, a wasan da suka yi da yammacin Alhamis.

Za dai a buga wasan karshe ne a ranar 18 ga Mayu, a filin wasa na St. Jakob-Park, da ke a birnin Basel na kasar Switzerland.