Man City ta firgita da Real Madrid — Waddle

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Dan wasan Real Madrid, Gareth Bale ne ya jefa kwallo daya tilo a ragar Man City

Tsohon dan wasan gefe na Ingila, Chris Waddle ya ce 'yan wasan Manchester City sun firgita da Real Madrid, a zango na biyu na wasan kusa da karshe da suka tashi 1-0.

Kusan za a iya cewa Real Madrid ce ta mamaye wasan, yayin da 'yan wasan Man City suka kasa katabus.

Dan wasan Real Madrid, Gareth Bale ne dai ya zura kwallon.

Daman dai a zangon farko, Manchester City ba ta iya cin Real Madrid din ba duk kuwa da cewa a gidanta aka taka ledar.

Sai dai kuma kociyan Manchester City, Manuel Pellegrini ya ce bai yi da-na-sanin doke su da Real Madrid din ta yi musu ba.