'Manyan 'yan wasan Leicester ku tsaya'

Image caption An sayi Riyad Mahrez a kan £400,000

Kociyan Leicester, Claudio Ranieri ya roki manyan 'yan wasan kungiyar da ka da su bar kulob din, har sai nan da shekara daya.

Ana dai kyautata zaton cewa sanannun 'yan wasan kungiyar kamar Jamie Vardy da Riyadh Mahrez da N'Golo Kante za su iya komawa wasu kungiyoyin a karshen kaka.

Ranieri ya ce " Ka da ku tafi. Idan kuka koma wani kulob din, to zai yi wuya a bar ku kuyi wasa."

An dai hada 'yan wasan Leicester ne a kan £57m, abin da ke nuna cewa kulob din shi ne yake da 'yan wasa mafi araha.