An haramtawa Dembele buga wasanni shida

Hakkin mallakar hoto Rex Features
Image caption Dembele ya tsokani Diego Costa

Hukumar ƙwallon ƙAfar Ingila ta FA, ta haramtawa ɗan wasan tsakiya na ƙungiyar Tottenham Mousa Dembele, buga wasanni shida sakamakon tsokanar faɗa da ɗan wasan Chelsea Diego Coasta.

An nuna Dembele ɗan ƙasar Belgium yana tsokane was Costa ido a yayin wasan da suka tashi ci 2-2 da Chelsea ranar Litinin.

Alƙalin wasa Mark Clattenburg bai yi masa wani hukunci ba a lokacin wasan.

Dambele ya ce ba zai yi jayayya da hukumar ba, don haka koci Mauricio Pochettino ba zai samu damar sanya shi a wasanni shida ba.

Ya buga wasanni 29 a kakar wasa ta bana, inda ya zura ƙwallaye uku a raga.