Gareth Bale zai yi jinya

Hakkin mallakar hoto pa
Image caption Bale ya zura kwallo 19 a gasar La Liga ta bana.

Dan wasan Real Madrid Gareth Bale ba zai yi buga wasan da kulob din zai yi da Valencia a gasar cin kofin La Liga ba sakamakon raunin da ya ji a gwiwarsa.

Bale, mai shekara 26, ya taimaka wa Real wajen yin nasara a kan Manchester City ranar Laraba, lamarin da ya sa suka kai zagayen karshe na gasar cin kofin Zakarun Turai, inda za su fafata da Atletico Madrid ranar 28 ga watan Mayu.

Real suna kan gaba a kokarin daukar kofin La Liga, inda suke bayan Barcelona da maki daya, kuma suna da ragowar wasa biyu da za su buga.

Wata sanarwa da ta fito daga kulob din na Real ta ce dan wasan "yana fama da rauni a gwiwarsa ta dama".

Bale ya zura kwallo 19 a gasar La Liga ta bana, sannan ya taimakwa wajen zura kwallo 10.