'Bala'i ne idan kungiya ba ta hudun farko'

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Pellegrini zai bar City a karshen kakar wasan bana

Kociyan Manchester City, Manuel Pellegrini, ya ce babban bala'i ne idan babbar kungiyar kwallon kafa ba ta kare a hutun farko ba a gasa.

Pellegrini ya kuma kara da cewar saukin ta kawai shi ne kungiyar ta lashe kofuna a kakar wasan da take yi.

A ranar 4 ga watan Mayu ne Real Madrid ta fitar da Manchester City daga gasar cin kofin zakarun Turai a wasan daf da na karshe.

City za ta kara da Arsenal a kokarin da take yi na ganin ta kare kakar wasan Premier bana a cikin matakin 'yan hudun farko.

Pellegrini ya ce idan baka kare a hudun farko ba a gasa zai iya zama bala'i, amma kuma dama-dama idan ka dauki kofin zakarun Turai ko FA ko kuma League Cup.

Chelsea wadda ta dauki kofin Premier bara tana mataki na tara a teburin bana, kuma ba za ta kare a cikin hudun farko a gasar bana ba.