Barcelona na daf da lashe kofin La Liga

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Ranar Asabar za a kammala gasar La Liga ta bana

Barcelona ta kusa daukar kofin Gasar La Liga Spaniya ta bana, bayan da ta ci Espanyol 5-0 a wasan mako na 37 da suka yi a ranar Lahadi.

'Yan wasan da suka ci wa Barcelona kwallayen sun hada da Lionel Messi da Luis Suarez, wanda ya ci biyu a karawar, da Rafinha da kuma Neymar.

Barcelona tana mataki na daya a kan teburin gasar ta kuma bai wa Real Madrid tazarar maki daya wadda ta ci Valencia 3-2.

Atletico Madrid ta barar da damarta ta daukar kofin bana, bayan da Levante ta doke ta da ci 2-1.

Barca za ta ziyarci Granada a wasan karshe a ranar Asabar, yayin da Deportivo La Coruna za ta karbi bakuncin Real Madrid.

Ga sakamakon wasannin mako na 37 da aka yi:
  • Levante 2 Atl Madrid 1
  • Real Madrid 3 Valencia 2
  • Celta de Vigo 1 Málaga 0
  • Eibar 1 Real Betis 1
  • Getafe 1 Sporting de Gijón 1
  • Las Palmas 0 Ath Bilbao 0
  • Real Sociedad 2 Rayo Vallecano 1
  • Sevilla 1 Granada CF 4
  • Villarreal 0 Deportivo de La Coruña 2