City ta barar da damar zama ta hudu a Premier

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Arsenal tana mataki na uku a teburin Premier

Manchester City ta tashi wasa 2-2 da Arsenal a gasar cin kofin Premier wasan mako na 37 wanda suka fafata a Ettihad ranar Lahadi.

Sergio Aguero ne ya fara ci wa City kwallo daga yadi na 18, kuma mintuna biyu tsakani Olivier Giroud ya farkewa Arsenal.

City ta ci kwallo na biyu ta hannun Kevin de Bruyne, yayin da Sanchez ya ci wa Arsenal tata kwallon ta biyu.

Da wannan sakamakon City za ta kasa samun tikitin shiga Gasar cin Kofin Zakarun Turai ta badi ko da ta doke Swansea idan har Manchester United ta cinye wasanta da West Ham da kuma Bournemouth.

Arsenal na bukatar maki daya a kan Aston Villa a wasan karshe na gasar ta samu damar buga Gasar ta cin Kofin Zakaru karo na 20 a jere.

Pep Guardiola ne zai maye gurbin Manuell Pellegrini a matsayin mai horar da tamaula a Ettihad a badi