Sakamakon gasar Firimiyar Nigeria mako na 15

Hakkin mallakar hoto NPFL Twitter
Image caption An buga gasar mako na 15 a gasar cin kofin Firimiyar Nigeria

Enyimba ta doke Niger Tornadoes da ci 2-1 a gasar cin kofin Firimiyar Nigeria wasan mako na 15 da suka yi a ranar Lahadi.

Sauran sakamakon wasannin da aka fafata Wikki Tourist ma 2-1 ta ci Nasarawa United, yayin da Kano Pillars ita ma ta doke Ikorodu United da ci 2-1.

Rangers da Shooting Stars tashi suka yi canjaras 1-1, Plateau United da Sunshine Stars kuwa babu ci suka tashi.

Rivers United kuwa doke Warri Wolves ta yi a da ci daya mai ban haushi, inda Lobi Stars ta ci MFM 1-0.

Tun a ranar Asabar Abia Warriors ta ci Giwa FC daya mai ban haushi.

Ga sakamakon wasannin mako na 15 da aka fafata:
  • Heartland 2-1 El-Kanemi
  • Plateau Utd 0-0 SunshineStars
  • Rangers 1-1 Shooting Stars
  • Wolves 0-1 Rivers Utd
  • Wikki 2-1 Nasarawa Utd
  • Akwa Utd 2-0 Ifeanyiubah
  • Lobi 1-0 MFM FC
  • Enyimba 2-1 Tornadoes
  • Pillars 2-1 Ikorodu Utd
  • Abia Warriors 1-0 Giwa FC