Southampton ta ci Tottenham 2-1

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Tottenham tana mataki na biyu a kan teburin Premier

Tottenham ta yi rashin nasara a hannun Southampton da ci 2-1 a gasar Premier wasan mako na 37 da suka fafata a ranar Lahadi.

Son Heung-min ne ya fara ci wa Tottenham kwallo a minti na 16 da fara tamaula, sai dai kuma a minti na 31 Steven Davis ya farke kwallon ya kuma kara ta biyu saura minti takwas a tashi daga fafatawar.

Da wannan sakamakon Tottenham ta hada maki 70 tana kuma mataki na biyu a kan teburi, Southampton kuwa tana mataki na shida da maki 60.

Tottenham za ta buga wasan karshe na gasar bana da Newcastle United, yayin da Southampton za ta karbi bakuncin Crystal Palace.