Kompany ba zai buga gasar nahiyar Turai ba

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption A karon farko City ta kai wasan daf da na karshe a kofin zakarun Turai

Vincent Kompany ba zai buga wa tawagar kwallon kafa ta Belgium gasar cin kofin nahiyar Turai ta bana ba, sakamakon raunin da ya yi.

Kompany ne da kansa ya sanar da hakan a shafinsa na sada zumunta na Facebook.

Dan wasan mai shekara 30, sai sauya shi aka yi a wasan da Real Madrid ta ci Manchester City 1-0 a gasar cin kofin zakarun Turai wasan daf da na karshe a ranar Laraba.

Kompany, kyaftin din Belgium da Manchester City, ya ji rauni a wurare daban-daban sau biyar a bana, inda ya buga karawa 22 daga 57 da ya kamata ya yi a kakar da ake buga wa.

Belgium tana rukuni tare da Italia da Sweden da Jamhuriyar Ireland a gasar cin kofin nahiyar Turai ta bana da Faransa za ta karbi bakunci.