CAF ta ci tarar Nigeria kan cunkoso a fili

Image caption Sama da 'yan kallo 40,000 ne suka shiga filin wasa a Kaduna

Hukumar kwallon kafa ta Afirka, CAF, ta ci tarar Nigeria kudi $5,000, saboda samunta da laifin cika filin wasa fiye da kima.

Hukumar ta samu Nigeria ne da laifin kasa samar da tsaro a filin wasa na Kaduna a lokacin da Super Eagles ta kara da Masar, a wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin Afirka.

CAF din ta yanke wannan hukuncin ne a zaman da kwamitin da'a da ladabtarwa na hukumar ya yi a Afirka ta Kudu.

Sama da 'yan kallon tamaula 40,000 ne suka shiga filin wasa na Ahmadu Bello, wanda ke cin mutane 15,000 a ranar 29 ga watan Maris, 2016.

Gwamnatin jihar Kaduna ce ta ba da umarnin a kalli wasan ba tare da an biya kudin shiga filin ba.

Super Eagles da Masar sun tashi kunnen doki 1-1 a karawar ta Kaduna, a kuma wasa na biyu da suka yi Masar ce ta lashe da ci 1-0.