Mai tsaron raga ta mutu a Kamaru

Image caption 'Yar wasan ta mutu ne kwana biyu bayan mutuwar fitaccen dan wasan Kamaru Patrick Ekeng.

Hukumar kwallon kafar Kamaru ta sanar da mutuwar mai tsaron ragar kungiyar kwallon kafar mata ta kasar Jeanine Christelle Djomnang.

Djomnang, mai shekara 26, ta mutu ne ranar Lahadi bayan ta fadi lokacin da take motsa jiki kafin wasan da kungiyar su ta Femina Stars Ebolowa za ta yi a kudanci kasar, kuma an garzaya da ita asibiti.

Hukumar kwallon kafar Kamaru ta ce rahotanni farko sun nuna cewa 'yar wasan ta mutu ne sanadin bugun zuciya, ko da ya ke har yanzu ana jiran sakamakon da asibiti zai fitar.

'Yar wasan ta mutu ne kwana biyu bayan mutuwar fitaccen dan wasan Kamaru Patrick Ekeng, wanda ke murza leda a kasar Romania.

Djomnang ta yi korafin cewa tana fama da ciwon kirji gabanin mutuwar ta.