Ranieri ne kociyan da ya fi fice a Italiya

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption A karon farko da Leicester City ta lashe kofin Premier tun shekara 132 da aka kafa kungiyar

Kociyan Leicester City, Claudio Ranieri, ya lashe kyautar lambar yabo ta mai horarwa da ya fi yin fice a bana a Italiya.

Hakan ne ya sa aka karramashi da lambar yabo ta fitaccen kociyan tawagar kwallon Italiya, Enzo Bearzot.

Bearzot ya jagoranci tawagar Italiya lashe gasar cin kofin duniya ta 1982 wanda ya mutu a shekarar 2010.

A kuma shekarar 2011 aka tanadi kyautar, domin karrama mai horar da kwallon kafa dan Italiya da ya fi yin fice.

Raneiri ya jagoranci Leicester City lashe kofin Premier a karo na farko da kungiyar ta yi tun kafata da aka yi shekara 132.