Platini zai sauka daga shugabancin Uefa

Hakkin mallakar hoto Rianovosti
Image caption Platini ya gaza shawo kan kotu ta sauya hukuncin da Fifa ta yi masa.

Shugaban Uefa Michel Platini zai sauka daga shugabancin hukumar ta kwallon kafar Turai bayan ya gaza shawo kan wata kotu ta soke dakatarwar da aka yi masa daga shiga harkokin kwallon kafa.

Fifa ce dai ta dakatar da Platini daga shiga harkokin wasannin kwallon kafa na shekara shida, sannan ta dakatar da tsohon shugabanta Sepp Blatter shi ma tsawon shekara tara bisa zarginsu da hannu a cin hanci.

Sai dai sun musanta zargin.

A ranar Litinin kotun da ke kula da harkokin wasanni ta rage dakatarwar da aka yi wa Platini zuwa shekara shida.

Amma hukuncin bai yi masa dadi ba, lamarin da ya sa ya ce zai sauka daga shgabancin Uefa.