Man United za ta ziyarci West Ham

Image caption Man United tana mataki na biyar a teburi, West Ham tana ta bakwai

West Ham United za ta karbi bakuncin Manchester United a kwantan wasan gasar cin kofin Premier a ranar Talata.

Kungiyoyin biyu sun kara a wasan Premier a ranar 5 ga watan Disamba, inda suka tashi 0-0 a Old Trafford.

A kuma Old Trafford din United ta karbi bakuncin West Ham a gasar cin kofin FA wasan daf da na karshe ranar 13 ga watan Maris, inda suka yi kunnen doki 1-1.

A ranar 13 ga watan Afirilu United ta bakuncin Upton Park, inda ta ci West Ham 2-1.

Manchester United tana mataki na biyar a kan teburin Premier da maki 63, yayin da West Ham keda maki 59 kuma ta bakawi a teburin gasar.